?>

‘Yan Takara Uku Zasu Fafata A Zaben Kasar Siriya

‘Yan Takara Uku Zasu Fafata A Zaben Kasar Siriya

A kasar Siriya, ‘yan takara uku ne ke shirin fafatawa a zaben shugabancin kasar na ranar 26 ga watan nan.

ABNA24 : ‘yan takaran sun hada da shugaba mai barin gado Bashar Al’Assad da, Abdallah Salloum Abdallah, wani tsohon ministan kasar sai kuma Mahmoud Mareï wanda ake wa kallon dan adawa mai sassauci ra’ayi.

‘Yan takara 51 ne suka ajiye takardun takara a zaben, saidai kotun tsarin mulkin kasar ta yi wasi da sauren duk da cewa suna da damar daukaka kara.

Shugaba Bachar el-Assad, wanda ya gaji mulki daga mahaifinsa, ya kwashe shekara 21 yana mulkin kasar ta Siriya, kuma yanzu haka yana neman wa’adi na hudu.

Dan shekara 55, Bashar Al’Assad ya lashe zaben shugabancin kasar na 2014, da sama da kash1 88 cikin dari na yawan kuri’un da aka kada.

Siriya dai ta kwashe shekara 10 tana fama da yaki, sai kuma matsalar tattalin arziki sai kuma annobar korona wacce ta kara dagula al’amuran tattalin arzikin kasar.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*