?>

‘Yan Bindiga Sun Sace Wasu ‘Yan Кasashen China Da Mauritaniya A Mali

‘Yan Bindiga Sun Sace Wasu ‘Yan Кasashen China Da Mauritaniya A Mali

Rundunar sojin ƙasar Mali ta ba da sanarwar cewa wasu mahara sun sace wasu ‘yan ƙasar China su uku da kuma wasu ‘yan ƙasar Mauritaniya su biyu a wani wajen da ake aikin gine-gine a kudu maso yammacin ƙasar ta Mali.

ABNA24 : A wata sanarwa da ta buga a shafinta na Facebook, rundunar sojin Mali ɗin ta ce maharan sun kai harin ne a wannan wajen da ke kimanin kilomita 55 daga garin Kwala inda suka yi awun gaba da wasu motocin ‘a kori kura’ guda biyar tare da wasu mutane da suka yi garkuwa da su.

Har ila yau kuma maharan sun lalata wasu kayayyakin aiki da suke wajen mallakin kamfanin gine-gine na ƙasar China COVEC da kuma wani kamfanin gina hanyoyi na ƙasar Mauritaniya da ke aiki a yankin.

Har ila yau wani jami’in sojin ƙasar Mali ɗin ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa mutanen da aka yi garkuwa da su ɗin suna aiki ne na gina hanyoyi da ake yi a yankin, yana mai cewa a halin yanzu babban abin da sojojin suka sa a gaba shi ne hanyar da za a bi wajen ƙwato mutanen da aka yi garkuwa da su ɗin.

Har yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗau alhakin satar mutanen, to sai dai kamfanin dillancin labaran Al-Akhbar na ƙasar Mauritaniyan ya ce maharan sun zo ne a kan Babura inda suka ƙona kayayyakin da suke wajen kafin kuma suka yi gaba da mutanen, a wani abu da yayi kama da irin yadda ‘yan ƙungiyar ta’addancin da suke cin karensu babu babbaka a ƙasar Malin suke yi.

Tun a shekara ta 2012 ne dai ƙasar Mali ɗin take fama da hare-haren ta’addancin da ƙungiyoyin Al-Кa’ida da ISIS da sauran waɗanda suke da alaƙa da su suke aikatawa a ƙasar lamarin yan zuwa yanzu yayi sanadiyyar mutuwar dubban mutane a ƙasar.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*