?>

​Zulum: ‘Yan Ta’adda Sun Sake Kwace Iko Da Kananan Hukumomi 2 Na Jihar Borno

​Zulum: ‘Yan Ta’adda Sun Sake Kwace Iko Da Kananan Hukumomi 2 Na Jihar Borno

Gwamnan Borno Babagana Zulum, ya ce kananan hukumomi biyu da suka hada da Abadam da kuma Guzamala sun koma karkashin ikon mayakan ISWAP, tsagin da ya balle daga kungiyar ‘yan Boko Haram.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Zulum ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da kwamitin majalisar dattawa kan harkokin soji, wanda ya kai masa ziyarar a Maiduguri, ranar Laraba.

Yayin da yake yabawa gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da hukumomin tsaro bisa nasarorin da aka samu a Borno, Zulum ya ce ya damu matuka game da karuwar mayakan ISWAP a sassan jihar, musamman daga bangaren kudanci, inda ya kara da gargadin cewa bangaren na ISWAP sun fi na Boko Haram karfi da kuma makamai.

Gwamnan ya koka kan cewar idan ba a gaggauta daukar mataki ba, barzanar na iya zama illa ba ga mutanen arewa maso gabashin Najeriya kadai ba, har ma da kasa baki daya.

Farfesa Babagana Zulum ya ce a watannin baya bayan nan jiharsa ta samu kwanciyar hankali musamman a fannin noma sakamakon mika wuya da ‘yan tada kayar baya da dama suka yi ga sojoji.

A cewarsa, tun bayan da mayakan suka mika wuya, an samu karuwar noma gonaki da akalla kashi 700 cikin 100.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*