?>

​Yemen: Hare-Hare Kan Cibiyar Bada Ruwan Sha A Sa’ada Wanda Saudia Ta Yi Wani Babbar Laifin Yaki Ne

​Yemen: Hare-Hare Kan Cibiyar Bada Ruwan Sha A Sa’ada Wanda Saudia Ta Yi Wani Babbar Laifin Yaki Ne

Gwamnatin kasar Yemen ta yi allawadai da hare-haren da jiragen yakin kasar Saudiya da kawayenta suka kai kan cibiyar bada ruwan sha na lardin Sa’ada kuma ta bayyana shi a matsayin laifin yaki. Sannan ta bukaci MDD da kungiyoyin kare hakkin bil’adama a duniya su yi allawadai da wadannan hare hare.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta AL-Masira ta kungiyar Huthi ta nakalto ministan ruwa da kuma kula da yanayi Hanin Al-Darib yana cewa cibiyar tana bada ruwan shag a mutane akalla 130,000 a lardin na Sa’ada.

Har’ila yau jiragen yaki na Saudiya da kawayenta sun kai hari kan cibiyar bada ruwa na birbib Sa’ada mai mutane kimani 20,000 inda suka lalata ta.

Bayan da kasar Saudia da kawayenta sun kasa samun nasara kan sojoji da mayakan sa kai a fagen daga sun koma kan rugurguza cibiyoyin masu muhimmanci a kasar Yemen tare da jiragen yaki.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*