?>

​Wakilan Kasashe Da Kungiyoyin Masu Gwagwamaya Zasu Raya Ranar Qudus Ta Duniya A Tehran

​Wakilan Kasashe Da Kungiyoyin Masu Gwagwamaya Zasu Raya Ranar Qudus Ta Duniya A Tehran

Shugaban majalisar shura ta hukumar Tabligal–Islami a nan Tehran ya bayyana cewa a ranar Alhamis mai zuwa ce wakilai daga kasashe masu gwagwarmaya zasu raya ranar Qudus ta duniya, rana guda kafin jumma’a na karshe na watan ramalan ta wannan shekara.

ABNA24 : Majiyar muryar Jumhuriyar musulunci ta Iran ta nakalto Sayyeed Muhsen Mahmoodi shugaban majalisar shoora ta Tabligat Islami yana fadar haka , ya kuma kara da cewa wakilai daga kasashen Falasdinu, Yemen, Lebanon, Iraki zasu gudanar da taro a masallacin Imam Sadik (a) dake dandalin Falasdinu a nan tehran don fara taron raya ranar Qudus ta duniya.

Imam Khumaini (q) wanda ya kafa JMI ya ayyana ranar jumma’a ta karshe na kowani watan ramalan a matsayin ranar Qudus ta duniya, da manufar raya batun al-amarin Faladinawa da kuma birnin Qudus a matsayinsa na babban matsala da ta fi damun al-ummar musulmi.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*