?>

​Uganda Ta Kammala Bincike Kan Zabar Filayen Da Za Ka Kafa Tashar Nukiliya Ta Farko A Gabashin Afirka

​Uganda Ta Kammala Bincike Kan Zabar Filayen Da Za Ka Kafa Tashar Nukiliya Ta Farko A Gabashin Afirka

Gwamnatin Uganda ta sanar da kawo karshen binciken da ta ke yi na zabar filayen da ake bukata domin gina tashar nukiliya ta farko a kasar da kuma gabashin Afirka, yayin da take kokarin kara karfinta na samar da wutar lantarki sau da dama.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Hakan na zuwa ne a cikin wata sanarwa da Okasai Sidronios Obolot, karamin ministan makamashi na Uganda ya fitar ba tare da bayyana wurin takamaimai ba.

A nata bangaren, Alain de Closio, daraktan hukumar kula da makamashi ta kasa da kasa ta ce hukumar ta yi imanin cewa Uganda a shirye take ta gina tashar nukiliya.

A shekarar 2017, Uganda ta bayyana aniyar ta na gina tashar makamashin nukiliya mai karfin megawatt 2,000.

Kafar yada labarai ta "Bloomberg" ta bayar da rahoton cewa, kasar Uganda, wadda ta dogara ne kan tashoshin samar da wutar lantarki, na neman kara yawan wutar lantarkin da take samarwa har sau 12 zuwa megawatt 17,000 a cikin matsakaicin lokaci, a cewar hukumar kula da wutar lantarki ta Uganda.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*