?>

​Tarayyar Turai: Ba Za Mu Yi Gaggawar Amincewa Da Mulkin Taliban A Afghanistan Ba

​Tarayyar Turai: Ba Za Mu Yi Gaggawar Amincewa Da Mulkin Taliban A Afghanistan Ba

Babban jami’in kungiyar Tarayyar Turai mai kula da harkokin nahiyar Asia ya bayyana cewa, ba za su yi gaggawar amincewa da mulkin Taliban a kasar Afghanistan ba, har sai kungiyar ta cika wasu sharudda na musamman.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a jiya a gaban mambobin majaliasar kungiyar Tarayyar Turai, babban jami’in kungiyar mai kula da harkokin nahiyar Asia Gunnar Wiegand ya bayyana cewa, ba za su yi gaggawar amincewa da mulkin Taliban a kasar Afghanistan ba, har sai kungiyar ta cika wasu sharudda na musamman da kungiyar za ta gindaya mata.

Gunnar Wiegand ya ce, babu wani tabbaci har yanzu kan makomar lamurra a kasar Afghanistan, kamar yadda kuma babu tabbaci kan ko Taliban za ta iya tafiyar da kasar Afghanistan, tare da mayar da lamurra yadda suke.

A kan haka ya ce, kungiyar Tarayyar Turai ba zata bude washafin alaka da kungiyar Taliban a hukumance ba, har sai kungiyar ta cika dukkanin sharuddan da za a kafa mata, kuma ta aiwatar da su a aikace.

Daga cikin sharuddan a cewarsa, akwai kare hakkokin ‘yan adam, da kuma bayar da dama ga kungiyoyin bayar da agaji na kasa da kasa su shiga Afghanistan a duk lokacin da suke so, tare da gudanar da ayyukansu cikin ‘yanci ba tare da wata takura ba.

Haka nan kuma yana daga cikin sharuddan cewa aka kafa gwamnati ta rikon kwarya, wadda za ta dukkanin bangarorin al’ummar kasar, baya ga haka kuma Taliban ta abyar da dama ga ‘yan kasar da suke bukatar ficewa daga kasar ba tare da an takura musu ba, da kuma rashin cutar da tsoffin jami’an gwamnatin da suka hambarar, sannan kuam kada Afganistan ta koma wata matattara ta ‘yan ta’adda.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*