?>

​Takht Ravanchi: Iran Ba Za Ta Amince Da Alkawulla Ba Tare Da Aiki Ba

​Takht Ravanchi: Iran Ba Za Ta Amince Da Alkawulla Ba Tare Da Aiki Ba

Wakilin Iran a majalisar dinkin duniya Majid Takht Ravanchi ya bayyana cewa, Iran din ba za ta amince da alkawulla na fatar baki ba tare da aiki ba.

ABNA24 : A cikin wani bayaninsa da kafofin yada labaran kasar Iran suka watsa a yau, wakilin Iran a majalisar dinkin duniya Majid Takht Ravanchi ya bayyana cewa, Iran din ba za ta amince da duk wasu alkalulla na fatar baki ba tare da aiki ba dangane da shirinta na nukiliya.

Takht Ravanchi ya ci gaba da cewa, yin alkawulla na fatar baki, ko rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyi na wani dan lokaci, hakan ba shi da wani alfanu ga Iran.

Ya ce dole ne Amurka da sauran bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar nukiliya, su yi aiki da dukkanin abin da suka rattaba hannu a kansa, da hakan ya hada da janye dukkanin takunkuman da Amurka ta kakaba wa Iran.

Ya ce bayan hakan kuma dole ne a samar da wata ka’ida wadda za ta lizimtawa kowane bangare yin aiki da abin da ke cikin yarjejeniyar, saboda abin da ya faru na keta alfarmar wannan yarjejeniya da gwamnatin Trump yi, wanda kuma babu tabbaci kan cewa hakan ba zai sake faruwa ba, ko da an cimma wata matsaya a yanzu.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni