?>

​Somalia: 'Yan Ta'addan Al-Shabab Sun Tayar Da Bam Tare Da Kashe Mutane Mogadishu

​Somalia: 'Yan Ta'addan Al-Shabab Sun Tayar Da Bam Tare Da Kashe Mutane Mogadishu

Mutane akalla 8 ne suka mutu sakamakon harin bam da aka kai da wata mota a kusa da filin sauka da tashin jiragen sama na Mogadishu babban birnin kasar Somaliya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar Russia Taoday ta bayar da rahoton cewa, karar fashewar bama-baman ta girgiza babban birnin kasar ta Somaliya a yau da rana tsaka, inda jama’a da dama suka kidime..

An dai kai harin ne a kusa da filin jirgin saman Mogadishu, a cewar majiyoyin gwamatin kasar.

Harin ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane takwas tare da jikkata wasu da dama.

Kungiyar ta'addanci ta al-Shabaab ta dauki alhakin kai harin kamar yadda ta saba yi, inda ta yi ikirarin cewa ta kai harin ne a kan wani ayarin motocin da ke dauke da wasu jami'ai farar fata.

Mohammad Abdi, jami'in tsaro a Mogadishu, ya ce an samu barna a wurin da fashewar ta faru, yana mai nuni da yiwuwar karuwar asarar rayuka.

Kungiyar Al-Shabaab da ke ikirarin kusanci da al-Qaeda, tana fafatawa da gwamnatin tsakiyar Somaliya tun shekara ta 2008, inda daga lokaci zuwa lokaci kungiyar ta kai munanan hare-hare a Mogadishu da wasu sassan kasar, tare da kashe mutane masu tarin yawa.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*