?>

​Shugaban Rasha Putin Ya Gana Da Takwaransa Na Falasdinu Mahmud Abbas Kan Batun Karfafa Alaka

​Shugaban Rasha Putin Ya Gana Da Takwaransa Na Falasdinu Mahmud Abbas Kan Batun Karfafa Alaka

Rahotanni sun bayyana cewa shuwagaban kasar Rasha Viladmir Putin da takwaransa na Falasdinu Mahamud Abbas Abu mazin sun gana a garin Sochi kuma sun tattauna game da yadda za su kara fadada dagantakar da ke tsakaninsu, da kuma halin da ake ciki a yammacin Asia. dukkan kasashen biyu sun amince su kara karfafa danganta ta fuskar tattalin arziki ala’adu da sauran bangarori.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kasar Rasha na kokarin shiga tsakanin kan batun falasdinu da zimmar ganin an kawo karshen rikicin da ake yi a yankunan fasladinawa da Israi’la ta mamaye, Abbas ya godewa Putin game da tsayin daka da yake yi wajen game da hakokin falasdinu.

Ziyarar ta shugaban gwamnatin kwarya kwaryan cin gashin kai ta Falasdinu tana zuwa ne bayan gayyatar da shugaban na rasha ya yi masa, masana sun yi amanna cewa shugaban na falasdinu na da kyakkyawan fata game da goyon bayan da take badawa wajen ganin an warare matsalolin da suke fuskanta.

Matsayin Rasha kan batun sasanta rikicin falasdinu da Isra’ila bai canza ba,bisa kudurin da kwamitin tsaro na majalisar dunkin duniya ya amince da shi na kafa kasashe biyu masu cin gashin kai domin amfanin alummomin yankin.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*