?>

​Shugaban Kasar Venezuela Zai Kawo Ziyarar Aiki A Nan Tehran

​Shugaban Kasar Venezuela Zai Kawo Ziyarar Aiki A Nan Tehran

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro tare da tawagar yan kasuwa da yan siyasa yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Iran don tattaunawa da jami’an gwamnatin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa shugaban kasar Iran Ibrahim Ra’isi ne ya gayyaci shugaba Madoro don kara karfafa dankon zumunci tsakanin kasshen biyu. Kafin haka dai kasashen biyu daga daga cikin kasashen da gwamnatocin kasar Amurka suka dorawa takunkuman tattalin arziki mafi muni a tarihin kasashen, don kifar da gwamnatocinsu.

Sannan gwamnatin kasar Iran ta taimakawa kasar ta Venezuela da jiragen ruwa na man fetur don farfado da tattalin arzikinta wacce ta rugurguje saboda takunkuman na Amurka. A wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shuwagabannin 2, shugaba Ra’isi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka tana adawa da kasashen Iran da Venezuela ne saboda ‘yancin kai da suke da shi. Da kuma rashin amincewa ga wata kasa ta shiga cikin lamuran cikin gida na kasashensu.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*