?>

​Shugaban Kasar Malawi Ya Dakatar Da Mataimakinsa Daga Ayyukan Gwamnati

​Shugaban Kasar Malawi Ya Dakatar Da Mataimakinsa Daga Ayyukan Gwamnati

Shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera ya kwace dukkan ayyukan gwamnati daga hannun mataimakinsa Saulos Chilima bayan da aka ambaci sunansa a cikin wadanda suka karbi cin hanci daga wani shugaban wasu kamfanoni a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shafin labarai na yanar gizo “africanews” ya nakalto shugaban yana fadar haka a jiya talata a waji jawabinda yayiwa mutanen kasar ta kafafen yada labaran gwamnati.

Shugaban ya dauki wannan matakin ne bayan da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar Anti-Corruption Bureau (ACB)’ ya bada sanarwan karin mutanen da suka karbi cin hanci da rasha daga hannun wani hamshakin dan kasuwa kuma mamallakin gungun kamfanoni wanda ake kira Zuneth Sattar.

Mr Sattar ya karbin ayyuka daban-daban daga hannun ma’aikatun gwamnatin kasar Malawi daga shekara ta 2017-2021 wadanda suka kai na dalar Amurka miliyon $150. Ya zuwa yanzu dai hukumar ACB tana tsare da jami’an gwamnati da fararen hula da tsoffin ministoci saboda badakkalar kwagiloli na Mr Sattar. Wadanda yawansu ya kai mutane 84 ya zuwa yanzu.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*