?>

​Shugaban Hukumar Nukiliya Ta Duniya Ya ce Bai Ga Wani Abu Da Ya Sabawa Doka A Shirin Nukiliyar Iran ba

​Shugaban Hukumar Nukiliya Ta Duniya Ya ce Bai Ga Wani Abu Da Ya Sabawa Doka A Shirin Nukiliyar Iran ba

A wani taron manema labarai na hadin guiwa da shugaban hukumar nukiliya ta Iran Mohammad Eslami ya yi da tawaransa na hukumar nukiliya ta Duniya Rafeal Grossi da yanzu haka yake ziyara a birnin Tehran, ya ce: ‘ masu sa ido na majalisar dinkin duniya sun bayyana cewa ba su ga wani abu da ya kaucema hanya a shirin Iran na nukiliya, kuma yayi dai dai da yarjeniyoyi da Kaidoji ayyukan nukiliya da aka amince da su.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Ana sa bangaren Mohammad Islami ya fadi cewa: “ babban abin da ke da muhimmanci game da batun dake tsakanin Iran da hukumar nukiliya ta duniya kan abin da ya shafi fasaha ne, don haka yana fatar hukumar ba za ta tasirantu da batutuwa na siyasa da makiya kasar Iran suke amfani da su wajen shafawa shirin nukiliyar Iran kashin kaji ba.

Majalisar shawarar musulunci ta kasar Iran ta takaita wuraren da sakataren hukumar IAEA zai kai cibiyoyinta na nukiliya domin mayar da martani game da janyewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar Iran a shekara ta 2018 kana kuma ta kakaba mata takunkumi mafi muni a tarihi.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*