?>

​Rwanda: An Kafa Dokar Hana Fita A Larduna 8 Da Birnin Kigali Domin Dakile Korona

​Rwanda: An Kafa Dokar Hana Fita A Larduna 8 Da Birnin Kigali Domin Dakile Korona

Gwamnatin kasar Rwanda ta bada sanarwan kafa dokar hana fita a larduna 8 na kasar tare da babban birnin kasar Kigali saboda dakile yaduwar cutar covid 19 a wadannan wurare.

ABNA24 : Jaridar ‘The News Times’ ta kasar ta bayyana cewa gwamnatin ta dauki wannan matakin ne bayan taron majalisar ministocin kasar a jiya Laraba.

Labarin ya kara da cewa dokar hana fitar za ta ci gaba da aiki har zuwa kwanaki 9 inda banda fita don ayyuka na lalura wadanda suka hada da sayan abinci da magunguna.

Har’ila yau dokar ta shafi manya-manya da kananan makarantu a wadannan yankuna in banda wadanda suke shirin daukar jarrabawar karshe.

Banda wannan gwamnatin ta takaita fita zirga-zirga a wasu yankunan daga karfe 6 na yamma har zuwa 4 na safe na tsawon wadannan kwanaki.

Ya zuwa yanzu dai mutane 10,761 suka kamu da cutar ta Covid 19 tun bayan bullarta shekaru biyu da suka gabata, a yayinda mutane 160 daga cikinsu suka rasa rayukansu.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*