?>

​Rasha: Za’a Tashi A Tattaunawar JCPOA NE A Inda Aka Tsaya

​Rasha: Za’a Tashi A Tattaunawar JCPOA NE A Inda Aka Tsaya

Jakadan kasar Rasha a cibiyoyin MDD da ke Vienna na kasar Austria ya bayyana cewa sabuwar tawagar kasar Iran wacce za ta ci gaba da tattaunawa kan dawowar Amurka cikin yarjejeniyar JCPOA, za ta tashi ne daga inda aka kwana a zama na karshe, wato na ranar 20 ga watan Yunin da ya gabata.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : ya nakalto Mikhail Auliyanuf jakadan kasar Rasha a Vienna ya na fadar haka a shafinsa na Twitter a jiya Lahadi. Ya kuma kara da cewa manufa itace akai ga inda ake bukata.

Kafin haka dai an gudanar da tarurruka har 6 bayan da gwamnatin Shugaba Biden na Amurka ta ce za ta dawo cikin yarjejeniyar JCPOA.

Babban sabanin da ke tsakanin bangarorin biyu dai, su ne da farko Amurka ta ce ba za ta dauke dukkan takunkuman da gwamnatin Trump ta dorawa kasar Iran bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar ba. Wanda bai sami amincewar kasar Iran ba.

Banda haka Iran ta bukace lamuni daga Amurka kan cewa ba za ta sake ficewa daga yarjejeniyar ba, wanda ita ma gwamnatin Amuka ta ki amincewa da hakan.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*