?>

​Rasha Da China Za Su Karfafa Ayyukan Hadin Gwiwa Na Soji, Makamashi Da Sararin Samaniya

​Rasha Da China Za Su Karfafa Ayyukan Hadin Gwiwa Na Soji, Makamashi Da Sararin Samaniya

Jakadan kasar Sin a kasar Rasha ya sanar da samun bunkasuwar hadin gwiwa tsakanin China da Rasha a fannoni daban daban da suka hada da soja da sararin samaniya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A wata hira da ya yi da kafafen yada labaran kasar Rasha a ranar Litinin din nan, jakadan kasar Sin a kasar Rasha ya sanar da bunkasa hadin gwiwa da kasar Rasha a fannin fasahar soja, makamashi da sararin samaniya.

shafin sadarwa na yanar gizo na China Morning Post cewa, Zhang Hanhui ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Tass cewa, makamashi shi ne mafi muhimmanci a fagen hadin gwiwa a aikace tsakanin Rasha da Sin, kuma za a karfafa irin wannan hadin gwiwa a sauran bangarorin da ake aiki tare tsakanin Rasha da China da suka hada da bangaren soja da sararin samaniya.

Zhang ya kara da cewa, akwai matsaloli a harkokin cinikayyar kasashen biyu, amma bangarorin biyu za su kara yawan kudaden cinikayyarsu don tabbatar da daidaito fannin ciniki, kuma ana sa ran nan da shekarar 2024, adadin cinikin zai kai dalar Amurka biliyan 200 tsakanin Rasha da China a cikin shkara guda.

Da aka tambaye shi ko takunkumin da Amurka da kasashen yammacin Turai suka kakaba wa Rasha na da hadari ga harkokin kasuwancin kasashen biyu, Zhang ya ce: Tabbas wadannan takunkuman za su haifar da matsala ga hadin gwiwa a zahiri tsakanin Sin da Rasha, kuma ya kamata kasashen biyu su karfafa sadarwa da yin hadin gwiwa don warware matsalolin da suka taso da suka da alaka da takunkumin cinikayya, tare da samar da wasu dabaru domin kaucewa illolin takunkuman.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*