?>

​Rahotanni: Daesh Ta Kafa Yankuna 4 A Tsakanin Iyakokin Libya Da Chadi

​Rahotanni: Daesh Ta Kafa Yankuna 4 A Tsakanin Iyakokin Libya Da Chadi

Rahotanni na cewa kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh ta kafa wasu yankuna 4 a tsakanin iyakokin kasar Libya da kuma kasar Chadi.

ABNA24 : Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, a yunkurin da kungiyar ‘yan ta’adda ta Deash take yi na sake farfadowa, a cikin yankunan arewaci da kuma yammacin Afirka, ta kafa wasu yankuna hudu a kan iyakokin Libya da Chadi.

Rahoton wanda kungiyar bincike kan harkokin tsaro ta nahiyar Afirka ta fitar, ya tabbatar da cewa akwai mayakan kungiyar Daesh da suke a cikin kasar Libya daga kasashen duniya daban-daban a yanzu haka, wanda kuma su ne suke kokarin fafada ayyukan kungiyar a cikin kasashen arewaci da yammacin nahiyar.

Kasashen da kungiyar daesh take kokarin karfafa karfinta a cikinsu a arewacin Afirkja sun hada da Libya, Aljeriya da kuma Tunisia, yayin da a yammacin Afirka kuwa kasashen sun hada da Najeriya, NIjar, Chadi, kamru, Mali, Burkina Faso.

Kungiyar Daesh ta samu wurin zama a cikin kasar Libya ne a cewar rahoton, bayan samun kungiyoyin ‘yan ta’adda masu akida irin tata, wadanda suka kame vyankuna suka shimfida ikonsu a cikin kasar ta Libya bayan kifar da gwamnatin Ghaddafi.

Yanzu haka dai wasu daga cikin kasashen da suka taimaka wajen kifar da gwamnatin Ghaddafi ne ake zargin cewa suna da hannu wajen taimaka ma wadannan ‘yan ta’adda, domin tabbatar da cewa kasar Libya bat a sake yin karfin da za ta gagare su ba, kamar yadda ta gagare su a lokacin mulkin Ghaddafi.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*