?>

​Raeisi: Yawan Man Da Iran Take Fitarwa A Halin Yanzu Ya Ninka Sau Biyu

​Raeisi: Yawan Man Da Iran Take Fitarwa A Halin Yanzu Ya Ninka Sau Biyu

Shugaban kasar Iran Ibrahim Raeisi ya ce, a halin yanzu danyen amn fetur da Iran take fitarwa ya ninka sau biyu, daga lokacin da ya hau karagar mulki a watan Agusta, duk da takunkumin da Amurka ta kakaba ma kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ibrahim Raeisi ya ce, Iran ta rubanya yawan danyen man fetur da take fitarwa domin sayar da shi a kasuwanninsa na duniya, kuma babu wata damuwa game da sayar da mai.

A cewar ministan man fetur Javad Owji, man da Iran ke fitarwa ya karu a karkashin takunkumi mafi tsauri ba tare da jiran sakamakon tattaunawar Vienna da ta tsaya cik a halin yanzu ba.

Ministan ya ce Iran ta dauki wasu matakai ne da wasu hanyoyi wadanda Amurka ba za ta iya saninsu ba, kuma komai yana tafiya yadda ya kamata ta hanyar cinikin mai tsakanin Iran da sauran bangarorin da take mu’amala da su.

Shugaba Raeisi ya ce harkokin cikikayya tsakanin Iran da kasahen ketare ya kai dala biliyan 100 a cikin kasa da shekara guda.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*