?>

​Putin: Za A Mika Makamin Sarmat Ga Rundunar Sojin Rasha Nan Da Karshen Shekara

​Putin: Za A Mika Makamin Sarmat Ga Rundunar Sojin Rasha Nan Da Karshen Shekara

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa za a mika makamin Sarmat ga rundunar sojin kasar nan da karshen wannan shekara.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wannan ya zo ne a cikin jawabin da Putin ya gabatar a yayin ganawarsa da daliban da suka kammala makarantun soji a birnin Moscow a ranar jiya Talata 21 ga watan Yuni.

Putin ya kara da cewa kowa ya san yanayin da ake ciki da kuma irin barazanar da Rasha take fuskanta, wanda hakan yasa ala tilas ta dauki dukkanin matakan da suka dace domin kare kanta da kuma tabbatar da wanzuwarta.

An kaddamar da gwajin farko na babban makami mai linzami na "Sarmat" daga Plesetsk cosmodrome a yankin Arkhangelsk na kasar Rasha a ranar 20 ga Afrilu.

Masana harkokin soji sun ce makami mai linzami samfurin RS-28 Sarmat da Rasha ta kera, zai iya daukar kawunan makaman nukiliya guda 10 a lokaci guda, tare da isar da su kowane sako na duniya a cikin kankanin lokaci, wanda ake kallonsa a matsayin mafi hadari a halin yanzu a duniya.

Wannan dai an zuwa sakamakon yadda takun saka k eta kara tsananta tsakanin Rasha da kasashen yammacin turai, musamman bayan fara ayyukan sojin da Rasha ke yia cikin kasar Ukraine, inda Rasha ta bayyana cewa NATO ta mayar ad Ukraine wani sansani da take amfani da shi domin cutar da kasar ta Rasha da al’ummarta.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*