?>

​Nijeriya: ‘Yan Bindiga Sun Sace Dakaci Da 'Yan Kasar Waje 2 A Zamfara

​Nijeriya: ‘Yan Bindiga Sun Sace Dakaci Da 'Yan Kasar Waje 2 A Zamfara

Kimani mako gud kenan da kissan mutanen kimani 200 a jihar Zamfara na arewa maso yammacin tarayyar Najeriya, ‘yan bindiga sun sace wani dakaci da matansa da kuma wasu ‘yan burkina Faso wadanda suke aikin hakar zinari a yankin nasu a jihar Zamfara.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa ‘yan bindigan sun farwa kauyen ‘Yar Kuka ne a ranar Litinin da yamma inda suka sace sarkin garin da matarsa da kuma dan’uwansa suka shiga da su daji. Wadanda aka sacen sun hada da Sarki Musa, Hadiza Musa da kuma Bawa Musa a jere.

Sai kuma a kauyen Kadauri ‘yan bindigan sun sace Mata 3 da badare gudu 3 a kauyen Kuzawa da ke karkashin lardin Kadauri a cikin karamar hukumar Maru na jihar ta Zamfara.

Wani mutumin kauyen mai suna Muhammad Tasiu ya fadawa Premioum times kan cewa ‘yan bindigan sun sace matansa 2 da yayansa mata 3.

A lokacinda Premium Times ta tuntubi Mohammed Shehu kakakin ‘yansanda na Jihar dangane da aukuwar wadannan hare-hare ya ce bai da labari.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*