?>

​Najeriya: Tawagar 'Yan wasan Olympic Ta Shirya Tsaf Domin Fara Wasanni

​Najeriya: Tawagar 'Yan wasan Olympic Ta Shirya Tsaf Domin Fara Wasanni

‘Yan wasan Najeriya da za su wakilci kasar a wasannin Olypic sun isa birnin Tokyo na kasar Japan a lokacin da ake shirye-shiryen bikin bude gasar ta Tokyo 2020.

ABNA24 : Gidan rediyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, ‘yan wasan Najeriya da suka isa Japan sun hada da ‘yan wasan kwallon tebur, da na motsa jiki, sai kuma wasan damben taekwondo da kuma na tsere.

Rukunin farko, wanda ya kunshi ‘yan wasa biyu, masu horarwa biyu da jami’ai shida, sun bar Abuja a ranar 6 ga watan Yuli, yayin da rukuni na biyu ya isa sansanin horonsu da ke yankin Kisarazu a ranar Laraba.

Rukuni na uku na 'yan wasa, wadanda suka kunshi 'yan wasan badminton da suka bar Najeriya a ranar 17 ga watan Yuli, za su hade da tawagar bayan an duba lafiyarsu.

Rukunin karshe, wanda ya hada da ministan wasanni, Sunday Dare, sun bar Najeriya a ranar jiya Litinin, yayin da kungiyoyin kwallon kwando maza da mata za su hade da tawagar Amurka zuwa Tokyo.

A ranar Juma’a 23 ga wannan wata na Yuli ne za a gudanar da bikin wasannin na Olympics a filin wasanni na Olympic da ke Tokyo fadar mulkin kasar ta Japan.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*