?>

​Najeriya: Mutane 869 Sun Kamu Da Korona A Jiya Laraba

​Najeriya: Mutane 869 Sun Kamu Da Korona A Jiya Laraba

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 869 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Laraba, sannan kuma mutum 8 suka rasu a dalilin Korona a wannan rana.

ABNA24 : Yanzu mutum 149,369 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 125,722 sun warke, 1,787 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 21,860 ke dauke da cutar a Najeriya.

Ranar Talata, mutum 1,368 suka kamu a Najeriya, jihohin Anambra, Oyo, Benue, Rivers da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.

Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko NPHCDA Faisal Shu’aib ya bayyana cewa za a yi wa mutum miliyan 109 allurar rigakafin cutar korona daga nan zuwa shekaru biyu masu zuwa.

Ya ce gwamnati na sa ran karbar kwalaben maganin rigakafin miliyan 57 daga AVATT da COVAX da kuma wasu miliyan 1.5, da 100,000 wanda kamfanin MTN da kuma kasar India suka baiwa Najeriya a matsayin gudunmawa, wanda za a yi amfani da su wajen yi wa wadanda suka dara shekaru 18 allurar rigakafi a Najeriya.

Wadanda za su kasancea sahun farko wajen samun allurar rigakfin dai su ne, Mata masu ciki, ma’aikatan kiwon lafiya, jami’an tsaro, tsofaffi da kuma marasa lafiya.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni