?>

​Najeriya: Ma’aikatar Noma Ta Mayar Da Martani Kan Hauhawar Farashin Kayan Abinci

​Najeriya: Ma’aikatar Noma Ta Mayar Da Martani Kan Hauhawar Farashin Kayan Abinci

Ma’aikatar noma ta Najeriya ta mayar da martani, dangane da zargin da ake yi kan cewa ita ce ta haifar da hauhawar farashin kayan abinci a kasar.

ABNA24 : A lokacin da yake mayar da martani kan wannan zargi, ministan ma’aikatar aikin gona da raya karkara ta Najeriya Alhaji Muhammad Sabo Nanono, ya bayyana cewa, sun saye kayan abinci a wasu manyan kasuwannin kasar domin adanawa a rumbunan tsimi na gwamnatin tarayya, domin fuskantar yanayi na karancin abinci ko da hakan ta faru a nan gaba.

Haka nan kuma ministan ya danganta hauhawan farashin kan manyan hukumomi na waje, manyan masu ruwa da tsaki a fannin faduwar darajar Naira da kuma kasashen da Najeriya ke makwabtaka da su.

Ya ce a halin yanzu sun sayi tan dubu 12 ne na abinci, wanda aka adana a cikin rumbun tsimi na gwamnatin tarayya, inda da farko sun niyar sayen tan dubu 100, amma kuma daga bisani ta fasa sayen wannan adadi mai yawa, saboda akwai bangarorin da suke bukatar sayen abinci, daga cikin hard a hukumomi na kasa da kasa, da suka hada da hukumar abinci ta duniya da kuma wasu hukumomin na daban.

Ministan ya ce yanzu haka sakamakon faduwar darajar Nairna, mutane daga kasashe makwabta suna shigowa cikin Najeriya suna kwasar abinci a cikin farashi mai arha, saboda yafi sauki a gare su idan suka canja kudadensu zuwa farashin naira.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*