?>

​Najeriya: Kungiyar Malaman Jami’o'i Sun Tsawaita Yajin Aikin Da Suke Yi Da Watanni 3

​Najeriya: Kungiyar Malaman Jami’o'i Sun Tsawaita Yajin Aikin Da Suke Yi Da Watanni 3

Kungiyar malaman jami’o’in gwamnati a tarayyar Najeriya ASSU ta tsawaita yajin aikin da take yi da wasu watanni uku. Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto shugaban kungiyar Emmanuel Osodeke yana fadar haka a safiyar yau Litinin, bayan da majalisar zartarwa ta kungiyar ta kammala taronta wanda ta fara tun jiya Lahadi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Labarin ya kara da cewa wannan na zuwa ne a dai-dai lokacinda daliban jami’o’I a duk fadin kasar suke zanga-zangar neman a warware matsalolin dake tsakanin gwamnati da malaman don su koma karatu.

Dalilan da kungiyar ta bayar na ci tsawaita yajin aikin dai sun hada da rashin cika alkarin da gwamnatin tarayyar ta daukawa malaman a baya.

Labarin ya kara da cewa babban abinda suke bukata shi ne gwamnatin tarayyar ta dauke tsarin bayan albashin malaman jami’a ta IPPIS don a maye gurbinsa da tsarin UTAS da aka saba.

Banda haka ASSU ta kara da cewa tana bukatar gwamnatin tarayyar ta aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma da kwamitin Munzali Jibrin ba tare da wani bata lokaci ba. Watanni uku kenan malaman jami’o’I na Nigeriya suka fara yajin aiki, saboda neman buyan bukatunsu.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*