?>

​Najeriya: Kungiyar Daliban Jami’o’ii A Najeriya Ta Bawa Gwamnatin Tarayyar Da ASSU Wa’adin Kwanaki 9 Na A Bude Jami’o’in Kasar

​Najeriya: Kungiyar Daliban Jami’o’ii A Najeriya Ta Bawa Gwamnatin Tarayyar Da ASSU Wa’adin Kwanaki 9 Na A Bude Jami’o’in Kasar

Kungiyar daliban jami’o’ii a tarayyar najeriya rashen kudu masu yamma da kuma rashen kudu masu gabacin kasar sun bawa gwamnatin tarayyar kasar da kungiyar kungiyar malaman Jami’o’ii kwanaki 9 na su bude jami’o’iin kasar ko kuma su dauki wasu matakai masu tsauri.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jaridar Leadership ta najeriya ta nakalto shugaban kungiyar NANS shiyar kudu masu yammacin kasar da kuma na kudu masu gabacin kasar Mr Moses Onyia suna fadar haka.

Daliban jami’o’iin sun yi barazanar rufe babban titin da ta hada biragen Lagos da Ibadan da kuma wasu tashoshin jiragen sama a yankin kudancin kasar don kowa ya ji a jika idan a ba’a warware matsalar jami’o’iin kasar ba.

Har’ila yau daliban jami’o’ii a kudu maso gabancin kasar ma sun yi irin wannan barazanar. A ranar litinin da ta gabata ce kungiyar malaman Jami’o’ii a tarayyar Najeriya suka karsa wasu watannin ukku a yajin aikin da suke yi, bayan yajin aiki na watanni uku. Daliban sun bayyana cewa gwamnatin tarayyar bata dauki matsalar yajin aikin malaman jami’o’ii da wani muhimmanci ba, a yajin aikin da suka fara tun ranar 14 ga watan Fabraini na shekara ta 2022 da muek ciki.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*