?>

​Najeriya: Gwamnatin Buhari Na Shirin Cire Tallafin Man Fetur Daga Shekarar 2022

​Najeriya: Gwamnatin Buhari Na Shirin Cire Tallafin Man Fetur Daga Shekarar 2022

Manajan Darakta na kamfanin mai na Najeriya NNPC Mele Kyari ya ce, farashin man na iya kaiwa naira N320 zuwa N340 kowanne lita daga shekara ta 2022 mai kamawa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kyari ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi a Abuja, inda yace tabbas babu abin da zai hana cire tallafin man a shekara mai zuwa, domin kuwa dokar da ake amfani da ita wajen biyan tallafin zata daina aiki daga karshen watan Fabarairu mai zuwa.

Shugaban kamfanin man yace a shekara mai zuwa babu wani tanadi da akayi na sanya kudin tallafin, kuma ganin yadda ayyuka suka yiwa gwamnati yawa, zasu aiwatar da shirin janye shi a cikin sauki.

Dangane da tashin farashin iskar gas da ake girki da shi kuwa, Kyari yace batu ne na karuwar bukatar sa ta haifar da hauhawan farashin tare da karancin sa a kasuwannin duniya.

Manajan Darakta na kamfanin NNPC ya ce, dama iskar gas bashi da wani tallafin da gwamnati take sanyawa, saboda haka farashin sa na tafiya ne da yadda kasuwar duniya take tafiya.

Kyari ya bayyana cewar kamfanin NNPC na iya bakin kokarin sa wajen kara yawan iskar gas din da ake sayarwa a cikin gida domin biyan bukatar masu aiki da shi.

Sai dai ita kuwa a nata bangaren ministar kudi, Zainab Ahmed cewa tayi gwamnati zata cire tallafin domin baiwa ‘Yan Najeriya matalauta naira N5,000 kowanne wata a matsayin abin da ta kira tallafin sufuri, wanda ta ce ‘yan Najeriya miliyan 30 zuwa 40 ake saran su ci gajiyar shiri da suke yi.

Wannan batu dai ya taso ne kasa da mako guda bayan shawarar da asusun bayar da lamuni na duniya ya baiwa Najeriya, kan cewa saboda basussukan da take ta ciwowa da hakan yasa bashi ya yi mata katutu a halin yanzu, ya kamata ta cire tallafin da take sanyawa a bangaren man fetur da ‘yan Najeriya suke amfani da shi, sannan kuma ta kara farashin kudin wutar lantarki a kasar.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*