?>

​Najeriya: Bashin Da Bankuna Suka Bayar Domin Bunkasa Tattalin Arziki Ya Haura Naira Triliyon 24

​Najeriya: Bashin Da Bankuna Suka Bayar Domin Bunkasa Tattalin Arziki Ya Haura Naira Triliyon 24

A ranar Talatar da ta gabata ce, Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa, ajimillar bashi daga bangaren bankuna ga tattalin arzikin Najeriya ya tashi zuwa naira tiriliyan 24.23 a karshen watan Mayu.

ABNA24 : Da yake magana a karshen taron yini biyu na Kwamitin manufofin kudi a Abuja, ya ce, “Dangane da haka, jimillar bashi a karshen Mayun wannan shekara ta 2021 ya tsaya a kan Naira Tiriliya 24.23, idan aka kwatanta da tiriliyan N22.68 a karshen Disamban 2020, inda karin da aka samu ya kai zuwa tiriliyan N1.55.”

Ya ce, a karkashin ayyukan ci gaba, bankin ya bayar da naira biliyan 756.51 ga kananan manoma 3,734,938 da ke noma hekta miliyan 4.6, daga cikin Naira biliya. 120.24, an kuna fadada shi zuwa daminar 2021 zuwa manoma 627,051 kan hekta 847,484, karkashin shirin tallafawa manoma na ‘Anchor Borrowers’.

Ya kara da cewa, game da shirin zuba jari a kananan da matsakaitan kasuwanci, Naira biliyan 121.57 aka raba ga mutane 32,617 wadanda suka amfana a cewarsa.

Sai dai wanan na zuwa nea daidai lokacin da ‘yan najeriya da dama suke cewa su dai har yanzu a cikin kafofin yada labarai dai kawai suke jin hakan.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*