?>

​Najeriya: An Sake Ceto Wasu Daga Cikin Daliban Da Aka Sace A Yawuri

​Najeriya: An Sake Ceto Wasu Daga Cikin Daliban Da Aka Sace A Yawuri

Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta ce ta sake ceto wasu dalibai biyu na sakandaren Birnin Yawuri ta Jihar Kebbi da ‘yan bindiga suka sace a watan Yunin da ya gabata.

ABNA24 : Tun farko dai rahotanni sun bayyana cewa mazauna garin Dandalla ne suka tsinci daliban na FGC Birnin Yawuri suna watangaririya a dajin Dansadau na Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara a ranar Asabar.

Sai dai da yake yi wa manema labarai jawabi a jiya Lahadi, Kwamishinan ‘Yan Sandan, Hussaini Abubakar ya ce jami’ansu ne suka yi nasarar ceto biyu daga cikin wadanda ‘yan ta’addan suka ce.

A ranar Asabar 31 ga watan Yulin da ya gata ne, dakarun rundunar ‘yan sanda ta musamman mai suna Operation Restore Peace suka yi nasarar ceto yaran, in ji Kwamishinan ‘Yan Sandan, Hussaini Abubakar.

Yaran biyu da ‘yan sanda suka ceto su ne Maryam ‘yar garin Wushishi da ke Jihar Neja, sai kuma Faruk wanda ya fito ne daga Wara da ke Jihar Kebbi. An ceto su ne daga wani daji da ke kauyen Babbar Doka a garin Dansadau.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*