?>

​Najeriya: ‘Yan ISWAP Sun Kashe Mutum 16 Da Sace Wasu ‘Yan Agaji 3 A Borno

​Najeriya: ‘Yan ISWAP Sun Kashe Mutum 16 Da Sace Wasu ‘Yan Agaji 3 A Borno

A kalla mutune 16 ciki har da mambobin jami’an tsaron sa-kai na CJTF ne suka rasa rayukansu a wasu jerin hare-haren da ake kyautata zaton mambobin mayakan ISWAP ne suka kaddamar a jihar Borno.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Har-ila-yau, an tattaro cewa, mayakan na ISWAP sun harbe masu sana’ar jari-bola 13 a kauyen Goni Kurmi da ke karamar hukumar Bama a jihar ranar Asabar.

Majiyoyin Jami’an tsaro sun shaida cewa, wadanda suka gamu da tsautsayin sun hada da maza 11 da mata 2.

Ya ce, mayakan sun zo cikin motoci hudu da kuma wasu a kan Babura inda suka mamaye yankunan tare da kaddamar da hare-haren su na ta’addanci.

Majiyoyi sun kuma kara da cewa, gomannin mutunen yankin sun arce domin tsira da rayukansu.

Kazalika, wasu mayaka dauke da muggan makamai da ake zargin ISWAP ne sun farmaki mambobin tsaron sa-kai na CJTF inda suka kashe uku daga cikinsu tare da yin garkuwa da ma’aikatan samar da agaji a karamar hukumar Monguno da ke Kudancin jihar Borno daren ranar Juma’a.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*