?>

​Mutane Shida Sun Mutu Sakamakon Wani Hari Da ‘Yan Tawaye Suka Kai Jamhuriyar Tsakiyar Afirka

​Mutane Shida Sun Mutu Sakamakon Wani Hari Da ‘Yan Tawaye Suka Kai Jamhuriyar Tsakiyar Afirka

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka sun bayyana cewar 'yan tawaye a ƙasar sun kashe mutum shida a wani hari da suka kai a arewa maso gabashin kasar.


ABNA24 : Wani mai magana da yawun rundunar da ake kira da MINUSCA, Laftanar Kanar Abdoulaziz Fall, ya shaida wa kamfanin labarai na AFP cewa sojojin gwamnati da ke zaune a Mann sun fuskanci hari daga wata kungiya da ake kira 3-R (Return, Reclamation, Rehabilitation).

Kakakin ya ƙara da cewa baya ga waɗanda aka kashe ɗin har ila yau kuma an raunana wasu mutane da dama.

Sai dai kuma ya ce a halin yanzu dai lamurra sun lafa a garin na Mann da ke kimanin kilomita 550 daga babban birnin ƙasar, Bangui.

Ita dai wannan ƙungiyar ta 3-R na daga cikin ƙungiyoyin mayakan sa-kai da aka kafa su a ƙasar wacce ta ke ci gaba da fuskantar tashin hankali mai tsanani cikin shekarun goman da suka gabata.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*