?>

​Masar: An Sake Kashe Wasu Sojoji A Wani Harin Ta’addanci A Yankin Sinai

​Masar: An Sake Kashe Wasu Sojoji A Wani Harin Ta’addanci A Yankin Sinai

Rundunar sojin Masar ta sanar da cewa an kashe wani babban jami'in soji guda tare da wasu kananan sojoji 4 da kuma jikkata wasu, a yayin farmakin da suka kai kan wasu gungun 'yan ta'adda a yankin Sinai.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Masar ta fitar ta bayyana cewa: Bisa la'akari da yadda dakarun kasar ke ci gaba da gudanar da ayyukan wanzar da tsaro da zaman lafiya a kasar, an fatattaki ‘yan ta’adda da dama.

Bayanin ya ce, an kuma yi kawanya ga wasu kebabbun wurare, da kuma daura da kan iyakokin kasar, inda sojojin saman kasar suka kai wani hari ta sama a ranar 7 ga watan Mayu, wanda ya yi sanadiyyar wargaza wasu sansanonin ‘yan ta’adda, tare da lalata wasu motoci guda biyu da ‘yan ta’adda ke amfani da su wajen aiwatar da shirinsu na ta’addanci, inda aka kashe 9 daga cikinsu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: Hakazalika sojojin sun yi nasarar gano tare da lalata wasu bama-bamai da aka yi niyyar kaiwa sojoji hari da su, kuma a safiyar jiya Laraba sojojin saman suka ci gaba da kai hare-haren na su, kuma an kashe ‘yan ta’adda akalla 7.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*