?>

​Martanin Azhar Kan Hare-Haren Ta’addanci A Iraki

​Martanin Azhar Kan Hare-Haren Ta’addanci A Iraki

Cibiyar ilimi ta Azhar ta yi tir da Allawadai da hare-haren ta’addancin da aka kai a kasar Iraki.

ABNA24 : A cikin wani bayani da ta fitar cibiyar ilimi ta Azhar ta sanar da cikakken goyon bayanta ga gwamnatin kasar iraki wajen yaki da ta'adanci a fadin kasar.

Bayanin na Azhar ya ce, masu kaddamar da hare-haren ta'addanci da sunan addini, abin da suke yi ba shi da wata alaka da addinin mulsunci, kamar yadda kuma ya yi hannun riga da 'yan adamtaka, a kan haka gwamnatin Iraki hakki ne a kanta ta yaki wadannan masharranta.

<p "="">Haka nan kuma Azhar ta mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren ta'addancin da aka kai kan lardin Salahuddin a ranar Asabar da ta gabata, inda jami'an tsaro da fararen hula suka rasa rayukansu, hare-haren da 'yan ta'addan takfir na Daesh suka dauki nauyin kaddamar da su.

A cikin kwanakin nan dai kungiyar daesh ta fara dawowa da hare-harenta na ta'addanci a kasar Iraki, wanda kuma hakan yana zuwa ne a daidai lokacin da al'ummar Iraki suke matsa lamba kan Aurka da ta fitar ad sojojinta daga kasar, yayin da kuma wasu bayanai na tsaro daga bangarori daban-daban a kasar ta Iraki suke yin ishara da cewa, Amurka tana da kyakkyawar alaka da kungiyar ta Daesh a cikin kasar ta Iraki.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*