?>

​Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Kasashen Dake Rikici Kan Tekun Nelu Da su Koma Teburin Tattaunawa

​Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Kasashen Dake Rikici Kan Tekun Nelu Da su Koma Teburin Tattaunawa

A wata takarda da kwamitin tsaro na MDD ya fitar ya bukace kasashen Masar Ethiopia da kasar Sudan da su koma teburin tattaunawar da kungiyar tarayyar Afrika ke jagoranta don kawo karshen takaddamar da suke ye game da gina madatsar ruwa da kasar Habasha ke yi akan tekun Nilu

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Zaman tattaunawar da kasahen suka yi a birnin Kinshasa a watan Aprilun da ya gabata an watse baram- baram ba tare da cimma wata matsaya ba, tun bayan da kasar habasha ta sanar da kammala bangare na biyu na ginin madastar ruwan da take yi aka kara samun zaman tankiya tsakaninta da kasar masar

Kasar Habasha ta bayyana cewa idan ta kammala gina madatsar ruwan za ta samar da karfin wutar lantarki da kai migawat 6000, yayin da kasashen Masar da Sudan suna nuna rashin amincewarsu da wannan aiki da suke ganin zai jawo musu koma baya sosai na ruwan da suke amfanin dashi,

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*