?>

​Majalisar Dinkin Duniya Na Kokarin Shiga Tsakani A Rikicin Sudan

​Majalisar Dinkin Duniya Na Kokarin Shiga Tsakani A Rikicin Sudan

A yau Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa za ta gayyaci shugabannin mulkin soja na Sudan da jam'iyyu da sauran ƙungiyoyi domin su shiga wani shiri na siyasa da zai kawo ƙarshen rikicin da ya biyo bayan juyin mulkin da aka yi a Oktobar bara.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shiga tsakani da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na ƴan makonni ya sa an mayar da Firaiminista Abdalla Hamdok kan muƙaminsa, sai dai ajiye aiki da ya yi a makon da ya gabata ya ƙara jawo damuwa da shiga halib rashin tabbas kan makomar siyasar Sudan da kuma batun miƙa mulki bayan zaben da ake sa ran za a yi a 2023.

Wakili na musamman na Majalisar Ɗinkin Duniya a Sudan Volker Perthes ya bayyana cewa duk matakan da aka ɗauka a baya har zuwa yanzu ba su yi aiki ba.

Ƙungiyoyi daban-daban dai da jam'iyyu sun gudanar da zanga-zanga inda suke cewa babu batun sulhu, zanga-zangar da ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 60.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*