?>

​Kenya: An Gudanar Da Jana'izar Babban Malmi Sheikh Abdullahi Nasser

​Kenya: An Gudanar Da Jana'izar Babban Malmi Sheikh Abdullahi Nasser

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da wannan taron janaza ne a yau 13 ga watan Disamba a gaban masoya Sheikh Abdullah Nasser da mabiya Ahlul Baiti (AS) a kasar Kenya, da kuma iyalansa da danginsa na jini.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - An haifi Sheikh Abdullah Nasser jagoran mabiya mazhabar ahlul bait na kasar Kenya a shekara ta 1932 a birnin Mombasa na kasar Kenya, kuma ya rasu yana da shekaru 90 a duniya.

Ya kasance babban mai tunani kuma ya ba da gudummawa sosai wajen rubuta littattafan addini.

Mutane da dama a Gabashi da Tsakiyar Afirka sun zama mabiya Ahlul Baiti ta hanyar karanta littattafan da ya rubuta.

Abdullahi Nasser, babban malami mai wa'azi ne a Mombasa, ya koma mabiyin mazhabar ahlul bait a shekarar 1975.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*