?>

​Kasar Rasha Ta Gwada Wani Sabon Makami Mai Linzami Mai Sauri

​Kasar Rasha Ta Gwada Wani Sabon Makami Mai Linzami Mai Sauri

Gwamnatin kasar Rasha ta bada sanarwan cewa ta gwada wani sabon makami mai linzami wanda saurinsa ya ninka saurin sauti akalla sau biyar.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa an gwada makamin ne daga jirgin yaki na ruwa masi suna Admiral Gorshkov a cikin tekun white sea kuma makamin ya sami bararsa mai tazarar kilomita 350 daga inda aka cilla shi.

Labarin ya kara da cewa makamin wanda shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yake kiransa ‘makamin da ba’a ganinsa’ , ana iya amfani shi daga kan motocin yaki a kan tudu, da kuma duk inda ake son amfani da shi.

Kasar Rasha tana ta samar da sabbin makami a cikin ‘yan shekarun da suka gabata don tabbatar da cewa ta kalubalanci barazanan makaman kasar Amurka a duk wani yakin da zai iya tasowa.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*