?>

​Jami’an Tsaron Yahudawa Sun Kame Falastinwa Da Dama A Birnin Quds

​Jami’an Tsaron Yahudawa Sun Kame Falastinwa Da Dama A Birnin Quds

Yahudawan sahyuniya sun kutsa kai a cikin masallacin Quds mai alfarma tare da keta alfamar masallacin.

ABNA24 : Rahotanni sun ce da jijjifin safiyar jiya ne yahudawan sahyuniya suka kaddamar da samame a cikin masallacin Quds mai alfarma, tare da keta alfarmar wannan masallaci.

Yahudawan sun shiga cikin masallacin ne da sunan suna raya ranar Tilmudi ta yahudawa, inda suke raya cewa a wannan rana ce aka rusa wurin ibadarsu da ke daidai wurin da aka gina masallacin quds.

Da dama daga cikin masana kwararru wadanda suka gudanar da bincike mai zurfi na tarihi sun karyata abin da yahudawan suke rayawa, domin kuwa abin da ya tabbata shi ne, babu wani abu da aka sani a wurin da masallacin Quds yake da yahudawa suke da'awa, tarihi bai tabbatar da haka.

Kamar kowane lokaci wannan samame da yahudawan suke kai wa kan masallacin Quds domin tsokanar musulmi, suna yin hakan ne tare da samu cikakkiyar kariya daga jami'an tsaron gwamnatin yahudawa ta Isra'ila.

Daruruwan falastinawa dai suka taru domin bayar ad kariya ga masallacin Quds, yayin da jami’an tsaron yahudawan Isra’ila suka yi amfani da kulake wajen lakada msuu duka, tare da jikkata da dama daga cikinsu da kuma kama wasu.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*