?>

​Jagoran Juyi Na Iran: Kasashen Yamma Na Amfani Da Batun Ukraine Domin Fadada NATO

​Jagoran Juyi Na Iran: Kasashen Yamma Na Amfani Da Batun Ukraine Domin Fadada NATO

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce kasashen yammacin duniya na amfani da batun Ukraine wajen share fagen kara fadada kungiyar tsaro ta NATO.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da shugaban kasar Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev a yammacin jiya Lahadi a birnin Tehran.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: “Wajibi ne a sanya ido sosai kan batutuwa mabambanta, sannan kuma mu yi taka tsantsan domin a ko da yaushe Amurkawa da yammacin turai suna neman fadada tasirinsu a yankuna daban-daban da suka hada da Gabashin Asia da kuma gabas ta tsakiya, domin murkushe ‘yancin kai da ikon wasu kasashe a wadannan yankuna.”

Jagoran ya kuma yi tsokaci mai zurfi game da alakar tarihi da al'adu tsakanin Iran da Kazakhstan, inda ya jaddada bukatar kara fadada hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu, musamman ma a fannin batutuwa da suka shafi yankin.

Har ila yau Ayatullah Khamenei ya yi kira da a kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu dangane da batutuwan siyasa da tattalin arziki, yana mai cewa ya zama wajibi a ci gaba da fadada huldar dake tsakanin kasashen biyu.

Yayin da yake jaddada wajibcin fara aiki da kwamitocin hadin gwiwa tsakanin Iran da Kazakhstan, jagoran ya ce dole ne kasashen biyu su kara himma wajen bin diddigi da aiwatar da yarjejeniyoyin da suka rattaba hannu a kansu.

A nasa bangaren, shugaban kasar Kazakhstan, ya ce ya yi tattaunawa da takwaransa na Iran, Ebrahim Raeisi mai matukar amfani.

Tokayev ya kara da cewa, bangarorin biyu sun rattaba hannu kan yarjeniyoyi, wadanda za su taimaka wajen kara fadada dangantakar kasashen biyu.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*