?>

​Isra’ila Da Masar Ne Suka Mara Baya Ga juyin Mulki A Sudan _ Maryam Al-Mahdi

​Isra’ila Da Masar Ne Suka Mara Baya Ga juyin Mulki A Sudan _ Maryam Al-Mahdi

Tsohuwar ministar harkokin wajen Sudan ta bayyana cewa, Isra'ila da Masar ne suka mara baya ga sojoji wajen yin juyin mulki a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A wata zantawa da wasu kafofin yada labarai na kasashen ketare, tsohuwar ministar harkokin wajen Sudan Maryam Almahdi ta bayyana cewa, Isra'ila da Masar ne suka mara baya ga sojoji wajen yin juyin mulki a kasar a cikin 'yan makonnin da suka gabata.

Da aka tambaye ta game da goyon bayan da kasashen waje suka yi kan matakin da babban hafsan sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan ya dauka a ranar 25 ga watan Oktoba, ta bayyana cewa galibin kasashen duniya sun bayyana rashin amincewarsu da juyin mulkin.

Ta kara da cewa: Hatta kasashen da suka nuna goyon bayan juyin mulkin, irinsu Masar, ba su iya fitowa fili suka bayyana goyon bayansu ba, kuma hakan ya faru ne saboda Allah wadai da juyin mulkin da Amurka ta yi.

Masar ta ba da sanarwar ta farko sa'o'i bayan yanke shawarar Al-Burhan na yin juyin mulki a ranar 25 ga Oktoba, a cikin wata sanarwa da ta fito daga ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Masar, inda ta bukaci dukkan bangarorin Sudan da su yi taka-tsan-tsan tare da ba da fifiko ga manyan muradu na kasa da fahimtar juna.

Dangane da matsayin gwamnatin Isra'ila kan ayyukan Al-Burhan kuwa, al-Mahdi ta ce: Gwamnatin Sudan tana sane da irin rawar da suke takawa wajen goyon bayan juyin mulkin soji, duk da cewa gwamnatin sahyoniyawan ta yi shiru.

Ko da yake a hukumance gwamnatin Isra'ila ta yi shiru game da abubuwan da ke faruwa a Sudan; Sai dai kafafen yada labaran Isra'ila sun ba da rahotannin ziyarar da wata tawagar Isra'ila ta kai birnin Khartoum a farkon wannan wata, inda suka gana da Al-Burhan, sannan Hamidati mataimakin shugaban majalisar rikon kwaryar kasar ya sake kai wata ziyara a Isra'ila.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*