?>

​Iran:Za’a Gudanar Da Zagaye Na 7 Na Tattaunawar Vienna Bayan Kafa Sabuwar Gwamnati

​Iran:Za’a Gudanar Da Zagaye Na 7 Na Tattaunawar Vienna Bayan Kafa Sabuwar Gwamnati

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Saeed KhadibZadeh ya bayyana cewa za’a ci gaba da tattaunawa dangane da dawowar Amurka cikin yarjejeniyar JCPOA bayan an kafa sabuwar gwamnati a nan kasar Iran.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press (IP) ya nakalto Saeed KhadibZadeh ya na fadar haka a wata hirar da ya yi da ‘yan jaridu ta kafar sadarwa ta internet a yau Litinin a nan birnin Tehran.

KhadibZadeh ya kara da cewa a cikin tattaunawan da suka gabata har zagaye na 6 an sami ci gaba mai yawa, sai dai ya kara tabbatar da cewa Iran za ta koma kan yarjejeniyar JCPOA ne kawai, idan Amurka ta dage dukkan takunkuman da aka dora mata bayan ficewarta daga yarjejeniyar a shekara ta 2018, sannan ta tabbatar da cewa an dage su ne, za ta koma kan yarjejeniyar.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*