?>

​Iran Ta Yi Kira Da A Saki Jami’inta Na Diflomasiyya Da Ake Tsare Da Shi A Belgium

​Iran Ta Yi Kira Da A Saki Jami’inta Na Diflomasiyya Da Ake Tsare Da Shi A Belgium

Iran ta yi Allah wadai da daure wani jami'in diflomasiyyarta a Belgium bisa wani zargi wanda wanda ba shi da tushe balantana makama.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A cikin watan Yunin 2018 ne hukumomin kasar Belgium suka ce ‘yan sandan kasar sun kama wata mota dauke da bama-bamai da kuma na’urar tayar da su, tare da yin ikirarin cewa Assadollah Assadi ne ya mika wadannan kayayyakin ga wasu mutane biyu.

Daga nan ne wata kotun kasar Belgium ta yanke hukuncin daurin shekaru 20 ga jami'in diflomasiyyar, wanda ke rike da mukamin mashawarci na uku a ofishin jakadancin Iran da ke Vienna, bayan da ta zarge shi da yunkurin kai hari kan kungiyar 'yan ta'adda ta Mujahedin-e-Khalq (MKO).

A ranar Talata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh ya ce tsarin tsare Assadi da shari'ar Assadi yana da kura-kurai kuma ya saba wa yarjejeniyar Vienna ta 1961 kan huldar diflomasiyya.

Khatibzadeh ya ce "an yi kira ga bangarorin Turai da ke da hannu a lamarin Assadollah Assadi da su gaggauta daukar matakin kawo karshen wannan batu.

Kalaman na kakakin ma’aikatar harkokin Iran sun zo ne bayan da wata kotun daukaka kara ta yi watsi da bukatun daukaka kara da wasu mutane uku suka gabatar, inda suke neman da a janye hukuncin da aka yanke a kan Assadi.

"Kamar yadda aka fada a baya, dukkanin tsare-tsaren shari'a, da kuma yanke hukuncin shari'a a kan Assadi sun faru ne gaba daya bisa keta yarjejeniyar Vienna kan huldar diflomasiyya," in ji shi.

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta mika kokenta a hukumance ga Austria da Jamus da kuma Beljiyam, tare da yin watsi da zargin da ake yi wa jami'in diflomasiyyar, tare da dagewa kan wajabcin sakinsa cikin gaggauwa," in ji Khatibzadeh.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*