?>

​Iran Ta Bukaci Hukumar IAEA Kada Ta Bari Manufofin Siyasar Wasu Kasashe Su Rinjayeta

​Iran Ta Bukaci Hukumar IAEA Kada Ta Bari Manufofin Siyasar Wasu Kasashe Su Rinjayeta

A wani taron manema labarai da ya gudana a yau litinin kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Sa'id KhadibZadeh ya yi kira ga hukuma mai kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA da kada ta bari manufofin siyasar wasu kasashen ya sa ta bata sunanta domin kawai cimma muradun siyasar kashin kai.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Da yake ishara game da ziyarar da Rafeel Grossi shugaban hukumar ta IAEA ya kawo nan Iran a yau litinin, KhadibZadeh ya kara da cewa yana fatan ziyarar ta zama mai ma’ana kamar ta bayanta.

Ya ce a kowanne lokaci muna shawartar hukumar ta tsaya a bangaren da ya shafi kayan aiki ka da ta bari wasu kasashe su yi amfani da sunanta don cimma manufofin siyasa da manufofin kashin kai.

Daga karshe ya ce Iran da sauran kasashen da ake tattaunawa kan shirin nukiliyarta suna bukatar samun tabbaci daga bangaren Amurka a Taron Biyanna da za’a yi a ranar 29 ga watan nuwamba ,ka da tarihi ya sake maimaita kansa ta yi abin da tsohon shugaban kasar Donlad Trumph yayi na ficewar daga yarjejeniyar a shekara ta 2015.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*