?>

​Iran: Shugaban Hukumar IAEA Na Gudanar da Ziyara A Yau A Tehran

​Iran: Shugaban Hukumar IAEA Na Gudanar da Ziyara A Yau A Tehran

Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta duniya yana gudanar da ziyarar aiki a yau a birnin Tehran na kasar Iran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A yayin wani taron manema labarai a birnin Tehran, wanda ya hada shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran Muhammad Islami, da kuma shugaban hukumar makamashin nukiliya ta duniya Rafael Grossi, bangarorin sun bayyana cewa cewa tattaunawa tana gudana a tsakaninsu kamar yadda aka tsara, tare da fatan cimma matsaya a yau a tsakaninsu.

Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran Muhammad Islami ya bayyana cewa, babu wani abu da ya saba wa ka’ida ko doka a cikin shirinsu na nukiliya, kamar yadda ita kanta hukumar makamashin nukiliya ta sha bayyana hakan a cikin rahotannin da ta fitar.

Ya ce sun cimma matsaya kan abubuwa da yawa da ake taddama a kansu tsakaninsu da hukumar IAEA a tattaunawar da shugaban hukumara yau a birnin Tehran, kuma yana fatan za a kammala tattaunawar ta yau tare da warware sauran batutuwan da suka rage.

Shi a nasa abangaren shugaban hukumar makamashin nukiliya ta duniya Rafael Grossi ya bayyaa cewa, ziyarar tasa da yake gudanarwa yanzu haka a Iran tana da matukar muhimmanci, kuma yana sa ran za a kammala warware sauran batutuwa da ake da sabani fahimta a kansu tsakanin hukumar ta IAEA da kuma hukumar makamashin nukiliya ta Iran a yau.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*