?>

​Iran: Kungiyar Taliban Bata Yi Aiki Da Alkawalinta Na Hana Noman Muggan Kwayoyi Ba

​Iran: Kungiyar Taliban Bata Yi Aiki Da Alkawalinta Na Hana Noman Muggan Kwayoyi Ba

Shugaban rundunar ‘yansanda masu yaki da shan kwayoyi na kasar Iran ya bayyana cewa gwamnatin Taliban ta kasar Afganistan bata cika alkawalin da ta dauka na yiki da noman wiwi da wasu tsirrai masu sa maye ba, kamar yadda ta yi alkawari bayan da ta karbi iko da kasar Afganistan wata guda da ya gabata ba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Majiyar muryar Jumhuriyar Musulunci ta Iran ta nakalto Majid Karimi yana fadar haka, ya kuma kara da cewa a shekarar da ta 1400 da ta gabata jami’an ‘yansandansa sun kama tun dubu 25 na ganye masu sa maye da kuma dangoginma wadanda aka shigo da su kasar Iran daga kasar Afganistan.

Karimi ya kara da cewa yawan kwayoyin da suka kama a shekara ta 1400 ya fi na sauran shekaru da suka gabata, wanda ya nuna cewa kungiyar Taliban bata yi koma dangane da hana noman wadannan kwayoyi ba, sai da fatan baki.

Gwamnatin JMI ta rasa rayukan ma’aikatanta ko kuma wadanda aka jiwa rauni daga cikinsu har 12,000 a cikin shekaru 40 da suka gabata.

Banda haka ita ce ta dukkan kasashen duniya yaki da miyagun kwayoyi a duniya, kasancewar kasar Afganistan wacce take makobtaka da it ace ta noman wadannan miyagun kwayoyi a duniya.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*