?>

​Iran: Dakarun IRGC Sun Kai Farmiki Kan Cibiyar ‘Yan Ta’adda A Garin Arbil Na Kasar Iraki

​Iran: Dakarun IRGC Sun Kai Farmiki Kan Cibiyar ‘Yan Ta’adda A Garin Arbil Na Kasar Iraki

Dakarun kare juyin juya halain musulunci a nan Iran sun kai farmaki kan sansanin ‘yan ta’adda a cikin yankin Kurdawan kasar Iraki dake arewa maso yammacin kasar Iran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jaridar “Sepah” News ta dakarun ta bada sanarwan cewa sojojin kasa ne suka kai hare-haren kan sansanonin ‘yan ta’addan wadanda suke shirin kai hare-haren ta’addanci a cikin kasar Iran.

Labarin ya kara da cewa kafin haka, dakarun sun kama ‘yan ta’adda biyar a garin Baneh a lardin kurdawan kasar Iran, inda garin bincike suka gano sansanonin yan ta’addan dake birnin Arbil babban birnin Lardin Kurdawa na kasar Iraki suka kuma wargaza sansanonin.

Labarain ya kara da cewa dakarun sun yi amfani da makaman atilary ne wajen kai hare haren a safiyar yau Laraba.

Kwamandan rundunar “Sayyushhadaa ta IRGC a yanklin arewa maso yammacin kasar Iran Burgediya Janar Majd Arjmanfard ya fadawa sepah news kan cewa gwamnatocin kasashen waje masu adawa da JMI suna amfani da yankin Kurdawan kasar Iraki mai kwaya-kwaryan cin gashin kai don gabatar da hare-haren ta’addanci a cikin kasar Iran.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*