?>

​Iran Da Syria Sun Kudiri Aniyar Kara Bunkasa Ayyukansu Na Hadin Gwiwa

​Iran Da Syria Sun Kudiri Aniyar Kara Bunkasa Ayyukansu Na Hadin Gwiwa

Gwamnatocin kasashen Iran da Syria sun kudiri aniyar kara bunkasa ayyukansu na hadin gwiwa a dukkanin bangarori.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wannan na zuwa a ziyar da shugaban kasar Syria Bashar Assad ya kai birnin Tehran ne fadar mulkin kasar Iran a jiya, inda ya gana da jagoran juyin juyin halin muslunci na kasar ta Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, da kuma shugaban kasar Ibrahim Ra’isi.

Bayan kammala ganawa da jagoran juyin juya hali, Shugaba Assad ya gana da shugaba Ra’isi a fadarsa da ke unguwar Sa’adat Abad da ke tsakiyar birnin Tehran, inda suka tattauna kan muhimman batutuwa da suke da alaka da kasashen biyu, ta fuskokin siyasa, harkokin tattalin arziki da cinikayya da kuma bunkasa masana’antu.

Ibrahim Ra’isi ya bayyana tsayin dakan da Syria ta yi wajen yin riko da ‘yanci da kuma dogara da ummarta, shi ne ya ba ta damar tsallakewa daga makirce-makircen da aka kulla mata domin rusa ta.

Ya ce a halin yanzu Syria ta dawo da karfinta acikin fagen siyasar yankin gabas ta tsakiya da kuma a fagen siyasar duniya, kuma kawancenta da kasashe masu ‘yancin siyasa yana kara karfi.

Shi am anasa bangaren shugaban kasar Syria Bashar Assad ya jinjina wa kasar ta Iran a kan dukkanin sadaukarwar da ta yi wajen taimaka ma Syria da al’umarta domin dakile makircin makiya, wanda hakan yana daga cikin manyan dalilan samun nasarar da kasar ta yi.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*