?>

​Iran Da Qatar Sun Jaddada Wajabcin Warware Matsalolin Gabas Ta Tsakiya Ta Hanyar Lumana

​Iran Da Qatar Sun Jaddada Wajabcin Warware Matsalolin Gabas Ta Tsakiya Ta Hanyar Lumana

Shugaban kasar Iran da sarkin Qatar sun jaddada wajabcin warware matsalolin yankin gabas ta tsakiya ta hanyar tattaunawa.

ABNA24 : A zantawar da ta gudana a daren jiya ta wayar tarho tsakanin shugaban kasar Iran Rauhani, da kuma sarkin kasar Qatar Tamim Bin Hamad Bin Khalifa Al Thani, sun yi wa junansu barka da idin babban sallah, da kuma fatan alhairi ga al’ummomin kasashen biyu da ma sauran al’ummomi na musulmia duniya.

Baya ga kuma sun wajabcin daukar matakai na warware matsalolin da suka addabi kasashen yankin gabas ta tsakiya ta hanyoyi na diflomasiyya da tattaunawa ta siyasa da fahimtar juna, maimakon yin amfani da karfin soji, ko wasu hanyoyi na cutar da juna.

Shugaba Rauhani ya bayyana cewa, matsayar kasarsa a bayyane take, kan fifita hanyoyi na sulhu da kuma zaman lafiya da juna a tsakanin dukkanin kasashen yankin tekun Fasha da kuma gabas ta tsakiya.

Shi ma a nasa bangaren sarkin kasar Qatar Tamim Bin Hamad Bin Khalifa Al Thani ya bayyana cewa, akwai kusanci matuka tsakanin mahangar Iran da Qatar kan yadda ya kamata a warware matsalolin yankin gabas ta tsakiya.

Ya ce bin wannan hanyar shi ne babban abin da zai kawo wanzuwar zaman lafiya a yankin da ci gaba da kuma bunkasar arziki, da kuma cin gajiyar dimbin arzikin da Allah ya huwace wa al’ummomin yankin.

Haka nan kuma ya yaba da irin gagarumin ci gaban da aka samu a cikin alakar da ke tsakanin Iran da Qatar a lokacin mulkin shugaba Rauhani.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*