?>

​Iran Da Oman Sun Jaddada Aniyarsu Ta Kara Habbaka Alaka A Dukkanin Bangarori

​Iran Da Oman Sun Jaddada Aniyarsu Ta Kara Habbaka Alaka A Dukkanin Bangarori

Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian ya yaba da dorewar dangantakar da ke tsakanin Iran da Oman, yana mai jaddada cewa fadada alaka da kasashen yankin tekun Fasha shi ne kan gaba a ajandar manufofin ketare na gwamnatin kasarsa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Amir-Abdollahian ya shaidawa manema labarai yayin da ya isa filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Muscat a ranar yau Litinin cewa, "A yayin ziyarar ta kwana guda, za mu tattauna kan ci gaban dangantakar kasashen biyu, shiyya-shiyya da kasa da kasa tare da jami'an Omani da kuma ministan harkokin wajen kasar Sayyid Badr al-Busaidi.”

Kyakkyawar makwabtaka da fadada mu'amala da kasashen da ke makwabtaka da mu su ne kan gaba a kan manufofin harkokin waje na gwamnatinmu a halin yanzu," in ji shi.

Daga nan ne ministan harkokin wajen na Iran ya yi ishara da yarjejeniyar zirga-zirgar ababen hawa tsakanin Iran, Oman, Turkmenistan, da Uzbekistan, yana mai bayyana fatan cewa nan ba da jimawa ba yarjejeniyar za ta fara aiki tsakanin kasashen da suka kulla yarjejeniyar.

Fahd bin Mahmoud Al Saeed, mataimakin sarkin kasar Oman, ya jaddada kusanci da ‘yan uwantaka a tsakanin kasashen biyu, da kuma ayyukan hadin gwiwa da ke tsakaninsu, da kuma yadda kasar Oman ke son taka rawa wajen dunkulewar kasashen yankin.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*