?>

​Iran: Bagheri Ya Gana Da Mataimakin Babban Jami’in Harkokin Wajen EU

​Iran: Bagheri Ya Gana Da Mataimakin Babban Jami’in Harkokin Wajen EU

Mataimakin babban jami'in harkokin waje na kungiyar Tarayyar Turai kuma mai kula da shawarwarin Vienna, Enrique Mora, ya gana da babban mai shiga tsakani na Iran Ali Bagheri a Tehran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wannan ita ce ziyara ta biyu da Mora ya kai Tehran a cikin watanni biyun da suka gabata.

Kafin tafiyarsa zuwa birnin Tehran, Mora ya ce zai gana da mai shiga tsakani na Iran Ali Bagheri Kani a wani yunƙuri na karfafa gwiwa domin ceto yarjejeniyar nukiliya ta 2015.

Mora ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa, "zan sake yin tafiya zuwa Tehran ne don ganawa da Bagheri Kani da sauran jami'ai kan tattaunawar Vienna da sauran batutuwa."

Yayin da yake magana kan tsarin tattaunawar a hukumance a babban birnin kasar Austria ya sheda cewa, "Aiki yana ci gaba domin ganin an cike gibin da ya rage a cikin wadannan shawarwari," in ji shi,.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh ya sanar a wani taron manema labarai cewa, ziyarar Mora a Tehran za ta gudana ne bayan tattaunawa ta karshe ta wayar tarho tsakanin Amir Abdollahian da Borrell, inda ya kara da cewa Mora zai gana da Bagheri a ziyarar tasa zuwa Tehran.

"Ziyarar Mora a Iran ta nuna cewa an samu ci gaba a kokarin da ake yi na aiwatar da shawarwarin da muka gabatar ta hanyar da ya kamata a bi, kuma duk da matakan adawa da wasu bangarori suka yi ta nuna domin wargaza wannan tattaunawa ta diflomasiyya, Iran da sauran bangarorin tattaunawar sun himmatu wajen ganin sun cimma daidaito da sahihiyar yarjejeniya," kamar yadda kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya ambata.

Khatibzadeh ya kara da cewa, idan har Amurka ta mayar da abin da ta karba daga gare mu, ta kuma amince da cewa ta tauye hakkin al'ummar Iran, to za mu iya komawa Vienna washegari bayan dawowar Mora, kuma ziyarar Mora a Tehran ta sanya wadannan shawarwarin a kan turba mai kyau.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*