?>

​Iran: An Cafke Wasu Ma’aikatan Mossad Da Ke Shirin Kashe Wasu Masana Kimiyyar Nukiliya

​Iran: An Cafke Wasu Ma’aikatan Mossad Da Ke Shirin Kashe Wasu Masana Kimiyyar Nukiliya

Wani babban jami'I a bangaren shari'a a Iran ya ce, an kame wasu ma’aikatan hukumar leken asiri ta Isra’ila Mossad, da suke shirin yi wa wasu masana kimiyyar nukiliya na kasar Iran kisan gilla.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Mehdi Shamsabadi, babban mai shigar da kara na yankin Sistan da Baluchestan a Iran ya shaida wa manema labarai a ranar jiya Talata cewa, kama wadannan jami'an na Mossad ya biyo bayan wani aiki na sirri mai sarkakiya da aka kwashe watanni takwas ana gudanarwa.

Ya kara da cewa, “An tattara kwararan hujjoji a kansu ta yadda ba su ma yi wani korafi ba a lokacin da aka kama su.

“Wadanda ake tuhumar sun amsa cewa wasu daga cikinsu sun yi hulda kai tsaye da jami’an Mossad,” a cewar jami’in na Iran.

Ya ce a halin yanzu ana kan bincike na farko a shari’ar kuma nan ba da jimawa ba za a shigar da kara a gaban kotu, domin kaddamar da tuhuma a kansua hukumance.

Sai dai jami’in ma’aikatar shari’ar na kasar bai yi karin haske kan mutanen da kuma kasashen da suka fito ba.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*